Talata 12 Mayu 2026 - 15:37
“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

Hauza/ Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na Imam Muhammad Baƙir Zone (Potiskum), sun rufe Mu'utamar da suka shiga mai taken “Gina Shakhsiyyar Matashi ɗan Gwagwarmaya”, karo na 14, a ranar Lahadi, 10 ga Mayu 2026, a garin Gashua, Jihar Yobe.

A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza da aka dauko daga shafin Facebook na Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na Imam Muhammad Baƙir Zone (Potiskum), sun rufe Mu'utamar da suka shiga mai taken “Gina Shakhsiyyar Matashi ɗan Gwagwarmaya”, karo na 14, a ranar Lahadi, 10 ga Mayu 2026, a garin Gashua, Jihar Yobe.

‎Da yake gabatar da jawabi a wajen taron, Shaikh Ahmad Ibrahim Potiskum, ya yi wa mahalarta taro nasiha kan gujewa aikata saɓon Allah da kuma rayuwa bisa tsoron Allah da wilaya. A cikin jawabinsa, ya kawo wani kyakkyawan misali daga Hadisin Imam Ali al-Ridha (AS), inda wani mutum ya tambayi Imam cewa: “Ya Imam, shin ku A’imma ba kwa yin saɓon Allah ne, ko kuwa kuna danne sha’awar yin saɓo ne idan ya zo ranku? Sai Imam (AS) ya tambaye shi cewa: 'Idan ka shiga bayan gida, shin ranka yana sha’awar cin najasar da ka fitar?' Mutumin ya amsa da cewa: A’a, ya Imam. Sai Imam (AS) Ya ce: 'Kamar yadda ranka yake tsananin ƙyamar hakan, haka mu ma A’imma muke ƙyamar sabon Allah, har ma fiye da haka.'”

‎Sheikh ya bayyana cewa wannan Hadisi yana koyar da yadda ya kamata mumini ya gina zuciyarsa wajen ƙin sabo da nisantar duk wani abu da zai fusata Allah. Sannan ya ci gaba da bayyana cewa duk wanda ya dogara ga Allah da gaske, Allah zai isar masa a kowane hali da kowane janibi, domin Allah na azurta wanda Ya so ba tare da iyaka ba. Ya ce mai Wilaya idan ya roƙi Allah wani abu, Allah zai ba shi idan akwai alheri a cikinsa.

‎Haka kuma, Malam ya yi jan hankali kan muhimmancin neman sani da nisantar ruɗun duniya. Ya ce "tun da Allah Ya yi wa mutum ni’imar Wilaya, bai kamata ya bari abin duniya ya shagaltar da shi ba, domin ya san daga ina ya fito kuma ya san inda zai koma."

A wani ɓangare na jawabinsa, Shaikh Ahmad ya yi kira ga matasa da su kasance suna zaɓar masu wilaya wajen aure, maza da mata, saboda muhimmancin hakan wajen gina kyakkyawar tarbiyya da kyakkyawar makoma ga ’ya’ya.

A ƙarshen jawabinsa, Sheikh ya jaddada muhimmancin tarbiyya da shawarwari kafin aure, yana mai cewa ya zama wajibi a riƙa wayar da kan matasa domin su san hakkokin juna da kuma yadda za su mutunta rayuwar aure. Ya bayar da misali da cewa mace ba baiwa ba ce, illa wata ’yar gata ce da ta taso cikin kulawa da tarbiyyar iyayenta, sannan daga baya ta koma gidan mijinta cikin daraja da mutunci, kuma idan tsufa ya zo kulawarta ta koma hannun ’ya’yanta.

‎Tun daga ranar Juma’ar da aka fara gabatar da wannan Mu’utamar, an gabatar da jawabai da shirye-shirye daban-daban da suka mayar da hankalin matasa 'yan gwagwarmaya ta fuskar neman ilimi, tarbiyya da kuma yadda matasa za su fahimci wasu al’amura da zamani ya zo da su.

‎Daga cikin jawaban da aka gabatar akwai jawabin Malam Nasiru Yusuf Zango mai taken “Ilimi a Matsayin Ginshiƙin Gudunmawar Matashi Ɗan Gwagwarmaya," inda ya yi bayani a kan muhimmancin neman ilimi domin matashi ya kasance mai anfani ga al’umma da gwagwarmaya baki ɗaya. Malam ya ce: “Akwai buƙatar matasa su samu ilimin da zai amfanar da kansa tare da al’umma baki ɗaya. Kamar yadda ba za a yi salla ba tare da alwala ba, haka kuma ba za a yi alwala ba tare da tsarki ba, sannan tsarki ba zai samu ba sai da ruwa. Haka rayuwar matashi ba za ta inganta ba sai da ilimi.”

‎Da ya ke nasa jawabin, Malam Adamu Jaji-Maji ya yi bayani kan “Haɗafin Harkar Islamiyya” inda ya yi ƙarin haske kan manufofi da ginshiƙan da Harkar ta ɗoro akansu. Ya ce “Harkar Musulunci ta ginu ne a kan manufofi da ƙa'idoji na hankali da Ilimi da ke jagorantar al’umma zuwa ga gwagwarmayar tabbatar da addini.” ya faɗi manufofi da Harkar Musulunci take a kansu, tare da kira ga matasa su fahimci manufar gwagwarmayar da suke ciki.

‎A cikin jawabinsa mai taken “Muhimmancin Haɗin Kai da Aiki Tare”, Dr. Magaji Manu ya bayyana cewa haɗin kai da fahimtar juna su ne manyan ginshiƙan da ke tabbatar da nasarar kowace gwagwarmaya. “Duk wata gwagwarmaya ba za ta kai ga nasara ba sai da tsayayyen manufa, haɗin kai da aiki tare tsakanin mambobinta.”

‎Haka kuma, Sheikh Muhammad Jiddah Nguru wanda shi ya yi jawabi ne a kan maudu'i mai taken “Tasirin Kafafen Sada Zumunta da Hanyoyin Amfani da Su wajen Gina Makomar Matasa”, inda ya bayyana yadda ya kamata matasa su yi anfani da kafafen sada zumunta wajen isar da saƙon da zai amfanar dasu. Sheikh ya ce: "Social media hanya ce ta isar da saƙo zuwa ga al’umma, sai dai kuma akwai hanyoyi da matakai da ya kamata a bi wajen isar da saƙon yadda ya dace. Abu na farko da ya kamata mutum ya fara yi kafin amfani da 'social media' shi ne fahimtar yadda ake amfani da ita da kuma manufar da za a yi amfani da ita a kai." 

‎Haka kuma, ya ce: "Idan mutum ya na son zama ɗan 'media', to wajibi ne ya nemi ilimi da ƙwarewa, domin aikin media aiki ne da ake gudanarwa bisa sani da karatu. Sannan ya ƙara da cewa idan mutum mai karanta rubuce-rubuce ne kawai a 'media', to ya tsaya a kan abin da ya fahimta, tare da guje wa yaɗa abin da bai da cikakken sani a kai.

A ɓangaren mata kuwa, Malama Hafsah Ɗahiru Ahmad ta gabatar da jawabai guda biyu masu taken “Yadda Ake Neman Aure a Musulunci” da kuma “Cikakken Hijabi a Musulunci”. A cikin jawabanta, ta yi cikakken bayani kan yadda Musulunci ya tsara rayuwar mata musamman ta fuskar mu’amala, tarbiyya da kiyaye ƙa’idojin addini a wannan zamani. Malama Ta ce: “Musulunci ya tanadi cikakkiyar hanya ta rayuwa ga mata, tun daga neman aure har zuwa kiyaye mutunci da cikakken hijabi.”

A cikin jawabanta kan “Yadda Ake Neman Aure a Musulunci” da “Cikakken Hijabi a Musulunci”, Malama Hafsah ta yi kira ga mata da su rungumi tarbiyyar da koyarwar addinin Musulunci domin samun rayuwa mai albarka da kuma kariya daga fitintinu na zamani da muke ciki.

‎A ƙarshe, bayan kammala dukkan wasu jawabai da aka gabatar a yayin Mu’utamar, an bada gyautar karramawa ga wasu daga cikin waɗanda suka yi fice wajen sadaukarwa da jajircewa a Dandalin Matasan Harkar Musulunci na wannan Zone.

Haka kuma, an karrama masu masauƙin baki bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ganin an kammala taron lafiya, inda aka ba su kyautar Kofi a matsayin nuna godiya da yabo. Daga nan kuma, an rufe taron da addu’a tare da sallamar kowa cikin farin ciki da fatan alheri.

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

“Ku Guji Saɓon Allah Kamar Yadda Kuke Ƙyamar Najasa"

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha